Najeriya ta kusa rushewa – Jaridar Financial Times

19

Jaridar Financial Times ta London ta bayyana Najeriya a matsayin kasar dake samun koma bayan tattalin arziki wacce matsaloli suka dabaibayeta irinsu ta’addanci da jahilci da fatara da sata da garkuwa da mutane, sannan ta na fuskantar barazanar rushewa matukar abubuwa basu hau kan saiti ba.

Jaridar wacce take Burtaniya, ta sanar da haka a ra’ayinta na yau.

Jaridar tace satar dalibai sama da 300 da aka yi a Kankara ta jihar Katsina, ya tunatar da yanmata 276 yan makarantar Chibok da aka sace a jihar Borno a shekarar 2014.

A cewar jaridar, ana kokonton ikirarin gwamnati na cewa ba a biya kudin fansa ba domin ceto yan makarantar Kankara.

Jaridar ta kuma dora alamar tambaya kan ikirarin shugaban kasa Muhammadu Buhari na cewa an karya lagon kungiyar Boko Haram.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

one × 1 =