Shugaban Buhari yayi alkawarin tallafawa zabe a Jamhuriyar Nijar

3

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayar da tabbacin cewa Najeriya zata bayar da gagarumar gudunmawa ga jamhuriyar Nijar wacce zata gudanar da zaben shugaban kasa da na yan majalisu a karshen watannan.

Shugaban kasar yayi jawabi a yau a fadar shugaban kasa dake Abuja, lokacin da yake karbar bakuncin tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo, wanda ya jagoranci tawagar ECOWAS masu sa ido a zaben kasar.

Wata sanarwa dauke da sa hannun kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, tace shugaba Buhari ya jinjinawa shugaban kasa Muhammadu Issufu saboda kin kokarin sauya kundin tsarin mulkin kasarsa domin karawa kansa wa’adin mulkin, bayan ya gama wa’adinsa na biyu.

Tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo, ya taya shugaban kasa Muhammadu Buhari murna saboda dawowar daliban da aka sace na makarantar sakandiren kimiyya ta gwamnati dake Kankara a jihar Katsina, da kuma murnar cikarsa shekaru 78 a duniya, a makon da ya gabata.

Yayi alkawarin cewa kungiyar ECOWAS zata tabattar da an gudanar da zabe na gaskiya cikin lumana a jamhuriyar Nijar, duk da kalubalen siyasa da na shari’a da na tsaro da ake fuskanta, inda ya kara da cewa tuni aka fara zaman ganawa tare da masu ruwa da tsaki.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two × five =