Shugaban Buhari ya gana da Gwamnan Borno dangane da rashin tsaro

6

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a jiya ya gana da gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum.

An gudanar da ganawar a sirrince a cikin ofishin shugaban kasa dake fadar Shugaban Kasa a Abuja.

Duk da kasancewar ba a sanar da dalilin ganawar ba, an yi amannar cewa ta ta’allaka ne akan batun rashin tsaro a jihar Borno.

Gwamnan bai zanta da maneman labaran fadar shugaban kasa ba, a karshen ganawar.

Kazalika, fadar shugaban kasa bata fitar da wata sanawar ba, dangane da ganawar, kawo lokacin hada wannan rahoton.

A ranar Asabar kadai, akalla mutane uku aka tabbatar an kashe a daya daga cikin kauyukan jihar Borno a yankin karamar hukumar Hawul, wanda yan Boko Haram suka kaiwa hari.

An bayar da rahoton cewa mayakan sun lalata makarantu da guraren ibada da sauran gine-gine a lokacin harin da suka kaiwa kayukan guda 4.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

six − 5 =