Buhari ya nanata jajircewar gwamnatinsa wajen kare rayuka da dukiyoyi a shekarar 2021

6

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace sace daliban makaranta a kasarnan ba zai cigaba da aukuwa ba, kasancewar gwamnatinsa ta jajirce wajen kare rayuka da dukiyoyin dukkan yan Najeriya.

Shugaba Buhari, wanda ya sanar da haka a yau a sakonsa ga yan Najeriya na sabuwar shekarar 2021 da aka yada, yace jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki sun nuna kwarewa sosai wajen sakin dalibai sama da 300 na makarantar Kankara da aka sace a bara.

Sai dai, Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya sanar da sakin dalibai 344, kwanaki 6 bayan mahara sun sace su.

Shugaba Buhari ya sha suka bayan sakin daliban, kasancewar yan Najeriya da dama da wasu kungiyoyi irinsu Afenifere, sun yi amannar cewa tsara sace yaran aka yi.

Sacen daliban na Kankara ba shine karon farko a tarihin kasarnan ba, ko a baya an taba sace daruruwan daliban makarantun yanmata na Chibok a jihar Borno da Dapchi a jihar Yobe.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

15 − thirteen =