Hukumar DSS ta yi zargin ana shirin taryar rikcin addini a fadin kasarnan

19

Hukumar tsaro ta DSS tace tana sane da shirye-shiryen wasu mutane na yunkurin tayar da rikice-rikicen addini a kasarnan.

Hukumar ta sanar da haka cikin wata sanarwa da kakakinta, Peter Afunanya, ya fitar a jiya da yamma.

Afunanya ya lissafa jihoshi 12 da aka nufa domin rikice-rikicen, inda ya umarci yan Najeriya da kauracewa duk wani yunkurin tashin-tashina.

Jihoshin sun hada da Sokoto, Kano, Kaduna, Plateau, Rivers, Oyo, Lagos da dukkan jihoshin yankin Kudu maso Gabas.

Yace hukumar tayi alkawarin hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da cewa an kiyaye doka da oda, inda ta shawarci wadanda ke shirin tayar da rikice-rikicen da su janye shirinsu.

Shawarar ta hukumar DSS na zuwa ne daidai lokacin da ake cigaba da samun karuwar rashin tsaro a wasu sassa na kasarnan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

six + 5 =