Yansanda a Kano sun tarwatsa gungun masu kwacen waya

6

Yansanda a Kano sun ce sun tarwatsa wani gungun masu kwacen waya, wadanda ake zargin suna satar waya a unguwannin Sharada da Sauna da Sabon Gari.

Kakakin yansanda na jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau yace jami’ai sun kama wadanda ake zargin a wani sumame daya biyo bayan korafe-korafen da mutane ke shigarwa dangane da karuwar kwacen waya a unguwannin da aka lissafa.

Haruna Kiyawa ya bayar da sunayen wadanda ake tsare dasu kamar haka Nura Muhammad dan shekara 18, Yusuf Dayyabu dan shekara 20, Nura Danladi dan shekara 20, Abdulkarim Abubakar dan shekara 18, Imrana Salisu dan shekara 19 da Friday Andrew dan shekara 20.

Sauran sune Mustapha Dahiru dan shekara 18, Ibrahim Salisu dan shekara 22, Najib Ibrahim dan shekara 28, Dahiru Abdullahi dan shekara 20, Ya’u Abdullahi dan shekara 20 da kuma Yusuf Sadiq dan shekara 18.

Kakakin na yansanda yace an kuma damke wasu shahararrun dilolin kwaya a lokacin sumamen.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

9 + 15 =