Jami’an zaman lafiya na MDD sun mutu bayan wani hari a Mali

1

Rahotanni daga Mali na cewa an kashe wasu dakarun wanzar da zaman lafiya uku na Majalisar Dinkin Duniya yayin wani hari da yan bindiga suka kai a kudancin garin Timbuktu.

An bayyana cewa dakarun yan asalin Ivory Coast ne da suka je kasar ta Mali aikin wanzar da zaman lafiya.

Harin ya faru ne da misalin karef 12 da rabi agogon GMT yayin da jami’an ke kan aiki.

An bayyana cewa motar jami’an ta taka nakiyar da aka binne, daga bisani kuma yan bindigar suka bude musu wuta, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Nan take aka kai jirage masu saukar ungulu da kuma jirgin daukar marasa lafiya domin kai wadanda suka samu raunuka zuwa asibiti.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

18 − 5 =