Yan bindiga sun sace mutane 18 a Kaduna

24

Akalla mutane 18, ciki har da iyaye mata hudu da jariransu, aka sace a wani samame da ‘yan bindiga suka kai a kauyensu a jihar.

Wannan dai shi ne na baya-bayan nan a cikin matsalar satar mutane a yankin.

‘Yan bindigar da ke kan babura sun afkawa kauyen Mando dake yankin karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar da sanyin safiyar jiya.

Mazauna garin sun ce an tafi da mutanen da aka sace zuwa wani daji.

Maharan sun kuma kwashe kayayyakin abinci daga kauyen.

Mai magana da yawun ‘yansanda na jihar, ya fadawa manema labarai cewa suna binciken lamarin.

Ba a bayyana wanda ya kai harin ba amma satar mutane don neman kudin fansa ta yi kamari a yankin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four + sixteen =