Gwamnatin Jigawa na kashe sama da N3.2bn kowane wata a matsayin kudaden gudanarwa

2

Gwamnatin jihar jigawa na kashe fiye da naira miliyan dubu 3 da miliyan 200 a harkokin gudanarwa na yau da kullum a kowanne wata daga cikin rabon arzikin kasa na naira miliyan dubu 3 da miliyan 500 zuwa naira miliyan dubu 4 da miliyan 500 da take samu daga gwamnatin tarayya.

Gwamnan Jiha, Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana haka a jiya yayin taro da manyan sakatarorin gwamnati da daraktoci a dakin taro na Ahmadu Bello a Dutse.

Ya kara da cewa gwamnatin jiha na kashe naira miliyan dubu 2 da miliyan 100 wajen biyan albashin ma’aikata, yayin da ake kashe naira miliyan 250 wajen ciyar da daliban makarantun kwana, da kuma naira miliyan 70 dake tafiya wajen ciyar da daliban makarantun firamare na kwana.

Haka kuma gwamnati tana kashe kudi naira miliyan 75 a harkokin lafiya matakin farko da naira miliyan 300 a matsayin kudaden tallafin karatu da jarrabawar NECO da WAEC, yayind a naira miliyan 100 ke tafiya a harkar bada ruwan sha da kuma naira miliyan 70 da ake rabawa ma’aikatu da hukumomin gwamnati a matsayin kudaden gudanarwa na yau da kullum.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

9 + seven =