Sojoji sun kashe yan bindiga 35 a jihar Zamfara

40

Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta Operation Hadarin Daji sun kashe yan bindiga masu fashin daji 35 a Zamfara tare da cafke mutane biyu.

Kakakin rundunar sojin ta Najeriya John Enenche a cikin sanarwar da ya fitar ya ce dakarun sun farwa yan fashin ne a yankin karamar hukumar Bungudu bayan samun labarin cewa yan fashin sun kora shanu, nan take kuma dakarun suka kai farmaki a jiya Lahadi inda suka kashe yan fashi 30 tare da kwato shanu 24 da kuma awaki.

Haka kuma rundunar ta ce dakarunta sun fatattaki yan bindiga da suka abkawa kauyen Janbako a karamar hukumar Maradun inda suka kashe yan bindiga biyar. Sanarwar ta kuma ce dakarun sun yi nasarar cafke wasu yan fashi biyu a kauyen Dungun Muazu a karamar hukumar Sabuwa da ke jihar Katsina.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 × 1 =