An samu adadi mafi yawa na wadanda suka kamu da corona a rana guda a Najeriya

16

A jiya ne Najeriya ta samu adadi mafi yawa na wadanda suka kamu da corona a rana guda bayan an samu mutane dubu 1 da 964 da suka harbu a fadin jihohi 23 da babban birnin tarayya.

Hakan yazo ne kasa da mako guda bayan bayan an samu adadi mafi yawa na baya na wadanda suka harbu a rana guda.

An samu adadi mafi yawa na baya a ranar 15 ga Janairu lokacin da aka tabbatar da samun sabbin mutane dubu 1 da 867 da suka kamu a jihohi 23 da babban birnin tarayya.

Cibiyar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ta tabbatar da sabbin mutanen da suka harbu a bayanin da ta wallafa a jiya, wanda yasa jiyan ta zama rana ta 18 a jere da ake samun sabbin wadanda suka harbu sama da dubu 1 a kasarnan.

A halin da ake ciki, mutane bakwai aka tabbatar sun mutu sakamakon cutar ta corona jiya a kasanrna, wanda ya kara yawan wadanda suka rasa rayukansu zuwa 1 dubu 485.

Kawo yanzu jumillar mutane dubu 116 da 655 suka harbu da cutar a duk fadin kasar, amma mutane dubu 21 da 542 ne suka jinyar cutar a halin yanzu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fifteen − twelve =