Gwamnatin Jigawa ta umarci ma’aikata su koma aiki

16
Gwamnan Jihar Jigawa Badaru Abubakar

Gwamnatin Jihar Jigawa ta umarci Ma’aikatan da ke matakin albashi na 12 zuwa kasa da su koma aiki daga yau.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Shugaban Ma’aikata na Jiha, Hussaini Ali Kila.

Ya ce tun lokacin da aka umarci ma’aikatan gwamnati da ke matakin albashi na 12 zuwa kasa da suyi aiki a gida a makonnin baya, abubuwa sun lafa kuma ma’aikatan suna bin ka’idojin kariya daga corona.

Ali Kila ya bayyana cewa dole dukkan ma’aikatan gwamnati su bi ka’idojin kariya daga corona da suka hada da amfani da abin rufe fuska, bawa juna tazara da kuma tsaftar jiki.

Ya ce shawarar ta biyo bayan cigaba da nasarorin da aka samu a yakin da ake yi da zagayowar annobar corona a karo na biyu a fadin jihar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 × two =