Jamuriyar Afrika ta Tsakiya ta ayyana dokar ta baci saboda yan tawaye

1

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta ayyana dokar ta baci yayin da wasu kungiyoyin yan bindiga dauke da makamai ke kokarin zagaye Bangui, babban birnin kasar.

Dokar zata dauki tsawon kwanaki 15 tare da baiwa hukumomi damar tsare wadanda ake zargi ba tare da izinin masu gabatar da kara ba.

Yanzu haka bangarorin ‘yan tawaye suna iko da mafi yawan kasar kuma suna kira ga shugaban kasar Faustin-Archange Touadéra da ya yi murabus, wanda ya lashe zaben kasar na watan Disamba.

A makon da ya gabata ne ‘yan tawayen suka kaddamar da hare-hare a kan unguwannin dake bayan babban birnin, amma suka janye bayan agajin da sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya suka kawo.

Jakadan Majalisar Dinkin Duniya ya roki karin sojoji daga Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.

Fadan ya tilastawa kusan mutane dubu 60 barin kasar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

15 + 9 =