Matsalar tsaro : Yadda aka ceto marayun da masu garkuwa suka sace a Abuja

12

Rahotanni daga ƙauyen Naharati da ke ƙaramar hukumar Abaji a babban birnin Abuja, na tabbatar da cewa an sako marayun nan da masu garkuwa da mutane suka yi awon gaba da su.

An samu nasarar kuɓutar da su ne bayan shafe tsawon kwanaki goma ana nemansu ruwa a jallo.

A ranar Larabar makon jiya ne, muka kawo muku rahoton sace yaran da ke zaune a wani gidan marayu tare da ƙarin wasu ƴan garin, bayan wani farmaki da masu satar mutane suka kai.

Shaidun da muka zanta da su sun bayyana wa BBC cewa sai da aka biya kuɗin fansa kafin a kai ga sako su.

Wani shaida da ya nemi mu sakaye sunansa ya bayyana mana cewa an biya naira miliyan biyu kafin a kai ga sakinsu, ko da yake ɓarayin sun riƙe wacce ta je kai kuɗin.

“Kamar mutanen da suka yi gudun yaƙi kwana da kwanaki basa ci basa sha, ƙila ma suna cin ciyawa, to haka muka same su, wasunsu ma a kafaɗu aka fito da su daga daji kafin mu sanya su a mota mu shigo gari da su,” in ji ɗaya daga cikin waɗanda suka karɓo su.

Ya ƙara da cewa ”Muna isowa gidan marayun wallahi wani daga cikinsu ya sassandarewa kai kace ya mutu, sai da aka riƙa rirriƙe shi saboda yadda ya fita daga hayyacinsa gaba ɗaya”.

Ya ce dukkansu yara ne ƴan makarantar Framare kuma yawanci mata sun fi yawa a cikinsu, sai guda ɗaya babba wadda take aji ɗaya na babbar sakandire da kuma wata guda dake aji biyu..

A cewarsa, yanzu suna asibiti ana ci gaba da kula da lafiyarsu, da alama za su ɗan ɗauki lokaci kafin su dawo hayyacinsu saboda baƙar wahalar da suka sha.

Da alama dama yankin ya jima yana fama da masu satar mutane, domin wasu majiyoyi sun ce ko da a makonni uku da suka gabata sai dai aka shigo yankin aka sace wasu mutane, wadanda aka sake su daga bisani bayan da aka biya kudin fansa.

Wani mazaunin garin ya bayyanawa BBC cewa da wuya a shafe mako ɗaya ba tare da masu satar mutane sun shiga yankin ba.

Lamarin satar mutane dai na ci gaba da ƙamari a Najeriya musamman a yankin arewacin ƙasar, inda wasu lokutan ma masu garkuwar ne ke dawowa da kansu su karbi kudin fansa bayan sun sace mutum.

Wani abu da aka saba jin hukumomi na cewa shi ne suna iyakacin bakin ƙoƙarinsu don shawo kan matsalar, amma har yanzu lamarin na ƙara ɓalɓalcewa.

BBC

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

16 − two =