Zaman duhu a Maiduguri yayin da ake zargin Boko Haram sun lalata hasumiyar wutar lantarki

49

Mazauna garin Maiduguri da kewaye sun shiga matsalar zaman duhu kiririn biyo bayan lalata daya daga cikin hasumiyar da ke samar da wutar lantarki ga birnin.

Rahotanni sun ce mayakane suka lalata hasumiyar a jihar da ke fama da rikicin Boko Haram.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ya ruwaito cewa, rashin wutar kwata-kwata da aka kwashe mako guda ana fama da ita, ya dakatar da sana’o’i da dama.

Wasu mazauna garin, wadanda suka zanta da manema labarai, bayan sun yi Allah wadai da abin da mayakan suka yi ba, sun kuma koka dangane da gazawar mahukunta wajen gyaran hasumiyar wutar.

Wani mai walda mai suna Moses Bala yace matsalar ta kawo karshen kasuwancinsa saboda ya dogara ne kacokan da wutar lantarkin don aikinsa.

Yayi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su hanzarta aiki don dawo da wutar lantarkin.

Musa Idris, Sahabi Abdulrahman, Amina Bello da Talatu Musa wadanda suma suka nuna bacin ransu game da rashin wutar lantarki a kan kananan sana’oinsu sun ce ba su san dalilin katsewar wutar ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

sixteen + three =