Ana cigaba da neman mutane 200 a India bayan ambaliyar ruwa ta kashe mutane 18

21

Ma’aikatan agajin gaggawa na neman mutane kusan 200 da har yanzu ba a gansu ba bayan wani dutsen kankara ya fada cikin kogi kuma ya haifar da wata mummunar ambaliyar ruwa a arewacin Indiya, inda mutane 18 suka mutu.

Ambaliyar ta fasa wata madatsar ruwa inda ruwa mai yawa ya malala zuwa wani kududdufi a jihar Uttarakhand a jiya.

Mafi yawa daga cikin wadanda suka bata din ana jin cewa ma’aikata ne daga kamfanonin samar da wutar lantarki guda biyu.

Aikin neman wadanda suka bata ya mayar da hankali kan gurare daban-daban, gami da wani bututu mai tsayin mita 200.

Fiye da mutane 30 ne suke makale a ciki lokacin da kwararar ruwan kankarar ya malale kududdufin, dauke da duwatsu da kasa.

Ba a samu ganawa da wadanda suka makale ba har yanzu. Kungiyoyin agaji suna fatan washe bututun da dare.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 × 2 =