Shugaba Buhari ya nemi a garanbawul a kungiyar Tarayyar Afirka

9

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi gargadin cewa kungiyar tarayyar Afrika zata tsaya cak, muddin bata mayar da hankali kan samun sakamako ba.

Shugaba Buhari, wanda yayi gargadin a lokacin da yake jawabi a wajen taron kungiyar tarayyar Afrika na wuni biyu, karo na 34, wanda ake gudanarwa, yayi kiran da za ayi cikakken garanbawul akan tsare-tsare da ayyukan kungiyar domin ta mayar da hankali wajen cimma manufofi.

Shugaba Buhari wanda ya yabawa Shugaba Paul Kagame na Rwanda saboda gabatar da rahoto na musamman da yayi akan bukatar yin garanbawul ga kungiyar ta tarayyar Afirka, ya kuma yabawa agajin shugabannin kasashen Afrika, bisa zaben Jakadan Najeriya, Bankole Adeoye, a matsayin kwamishinan harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro.

Shugaba Buhari yace yadda jakadan ya samu gagarumin goyon baya da kuri’u 55, yar manuniya ce cewa dukkan yayan kungiyar sun gudanar da zabe.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 + 13 =