Kowace jiha ta karbi N10bn daga gwamnatin tarayya – Gwamna Badaru

50
Gwamnan Jihar Jigawa Badaru Abubakar

Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana cewa kowacce daga cikin jihoshi 36 ta samu tallafi na kasafin kudi na naira biliyan 10 daga gwamnatin tarayya.

Gwamna Badaru ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a lokacin bikin aza harsashin ginin titin jirgin kasa daga Kano zuwa Katsina zuwa Maradi a cikin garin Katsina.

Gwamnan ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta tallafawa kowace jiha da naira biliyan 1 na tsawon watanni 10 domin basu damar sauke wasu nauye-nauyen da ke wuyansu.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin shugaba Buhari ta kuma tallafawa jihoshi da kudaden basukan da aka yafe, inda yace jihar Jigawa ta samu naira biliyan 40.

Ya kuma ce jihoshin sun samu wasu tallafin daga Shugaba Buhari kamar ba da rance da sauransu.

Hakanan ya tunatar da cewa kafin zuwan mulkin APC kimanin jihoshi 27 ne ba sa iya biyan albashin ma’aikata.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

seven + 9 =