Farfesa Abdallah Adamu ya sauka daga shugabancin jami’ar NOUN

7

Farfesa Abdallah Uba Adamu ya mika mulki ga Farfesa Olufemi Peters a matsayin sabon Shugaban Jami’ar Karatu Daga Gida, Open University.

Da yake jawabi a lokacin wani takaitaccen bikin mika mulkin, Farfesa Femi Peters ya godewa Allah da Ya tabbatar da hakan, yana mai cewa wannan tafiya ce mai kayatarwa tare da Farfesa Uba Adamu.

Ya yabawa Mataimakin Shugaban Jami’ar mai barin gado game da abubuwa da ya yi wa jami’ar.

Sabon Shugaban Jami’ar ya kuma sanar da cewa ya yi aiki tare da Farfesa Uba Adamu a matsayin tawagar wadanda suka shirya kafa jami’ar.

A jawabinsa na mika mulki, Farfesa Abdallah Uba Adamu ya ce shekaru biyar da suka gabata sun kasance masu tsananin gaske kuma sun ba shi damar bayar da gudummawar abin da zai iya, wajen fadada damar samun ilimi ga mutane a Najeriya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fourteen + one =