Buhari ya amince da kafa kamfani mai jarin N1 trillion domin samar da gine-gine

23

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kafa wani kamfani mai suna Infra-Co da hadin gwiwar yan kasuwa da zai samar da gine-gine, wanda za a zubawa jarin naira tiriliyan 1.

An yi hasashen cewa, zuwa wani lokaci jarin kamfanin zai karu zuwa naira tiriliyan 15.

Kamfanin zai kasance daya daga cikin manyan kamfanonin samar da gine-gine na farko a Afirka, kuma za a sadaukar da shi gaba daya ga cigaban gine-gine a Najeriya. An samar da kamfanin bisa wani tsari daga Majalisar Tattalin Kasa da Babban Bankin Kasa (CBN).

Shugaban Kasar ya nemi Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya shugabanci Kwamitin Gudanarwa da aka ba alhakin kafa kamfanin.

Jarin farko na kamfanin zai fito ne daga Babban Bankin Kasa da Hukumar Kula da Zuba Jari ta Kasa da kuma wani bankin samar da kudade na Afirka.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

thirteen − nine =