Buhari ya nada Adabayo a matsayin shugaban hukumar leken asirin tsaro

17

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada Manjo Janar Samuel Adebayo a matsayin shugaban hukumar leken asirin tsaro.

Adebayo, wanda ya karbi shugabancin hukumar a jiya daga hannun mataimakin shugaban hukumar, Manjo Janar Bolahan Oyefesobi, yayi alkawarin inganta ayyukan hukumar ta hanyar samar da kwararrun masana sirri.

Adebayo, wanda daraktan sirrin sojoji ne kafin nadinsa, ya nemi hadin kai da goyon bayan ma’aikatan hukumar, domin taimaka masa cimma muradun hukumar.

A cewarsa, dakarun sojin Najeriya sun samu nasarori da dama wajen magance matsalolin tsaro.

Adebayo yace wa’adin mulkinsa zai fi mayar da hankali wajen makasudin aikin hukumar na yunkurin leken sirri domin agazawa ayyukan tsaro da ake gudanarwa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fifteen − five =