Gwamnatin Tarayya ta bukaci yan Najeriya da su dena alakanta kabilanci da ayyukan bata gari

8

Gwamnatin tarayya ta bukaci yan Najeriya da su dena alakanta kabilanci da ayyukan bata gari a kasarnan.

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya bayar da wannan shawarar lokacin da ya karbi bakuncin wata tawaga daga makarantar harkokin tsaro, karkashin jagorancin kwamandanta, Ayodele Adeleke, a ofishinsa dake Abuja.

Aregbesola ya ankarar da cewa dole yan Najeriya su danganta tsaro da yadda kasashen duniya suke bayar da muhimmaci akan hakkoki cigaban bil’adama, inda ya kara jaddada cewa ayyukan bata gari masifa ce ga kasarnan.

Ya bukaci makarantar da ta taimakawa yan Najeriya wajen sauya yadda ake alakanta ta’addanci da wata kabila guda, lamarin dake kara rura wutar rikici da zaman dar-dar, babu gaira babu dalili.

Ministan yayi kira ga masu hannu da shuni da su taimakawa gwamnati wajen tallafawa marasa karfi a cikin al’umma, da nufin rage fatara da talauci, wanda a cewarsa, yana taimakawa matuka gaya wajen ayyukan ta’addanci a kasashe da dama a duniya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

15 + five =