Bankin CBN ya raba bashin naira biliyan 4 ga manoman shinkafa a Jigawa

5

Babban Bankin Kasa CBN ya bada rancen kayayyakin aikin nomana kusan naira miliyan dubu hudu ga manoman shinkafa karkashin shirin babban bankin na anchor barrower.

Babban jami’in kula da shirin na bankin a jihar Jigawa Abdu Amadu ya sanar da hakan a wajen bikin kaddamar da rabon kayayyakin aikin noman rani ga manoman shinkafa a jihar Jigawa

Yace babban bankin kasa ya bullo da shirin ne a 2015 da nufin tallafawa kananan manoma a fadin kasarnan.

Abdu Amadu ya kara da cewar gwamnatin jihar Jigawa ta biya basukan manoma na sama da naira miliyan dari bakwai ga bankin a madadin manoma sakamakon rashin ingancin Irin alkamar da aka raba musu.

Yayi kira ga maaikatu da hukumomi da kuma masu ruwa da tsaki dasu hada kai da bankin domin karbo basukan da nufin wasu su amfana

A nasa jawabin wakilin shugaban kungiyar manoman shinkafa na kasa Mallam Muhammad Auwal ya bayyana yi godiya ga gwamnati a madadin manoman shinkafa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three × 3 =