Liberia na cikin shirin kota kwana bayan barkewar Ebola a makociyarta Guinea

8

Shugaba George Weah na kasar Liberia ya sanar da cewa gwamnatinsa ta sanya hukumomin kiwon lafiya cikin shirin ko ta kwana sakamakon barkewar cutar Ebola a kasar Guinea mai makwabtaka.

Wannan ya zo ne kwana guda bayan da Ministan Kiwon Lafiya na Guinea Remy Lamah ya ce mutane hudu sun mutu daga cutar a garin Gouecke, kusa da iyakar arewa maso gabashin Liberia.

Shugaban na Liberia ya tabbatarwa da jama’a cewa ba a samu cutar Ebola a kasar ba kuma gwamnatinsa na yin duk mai yiwuwa don kare mutane daga cutar.

Cutar Ebola na iya yaduwa yayin da mutane suka yi mu’amala da jinin da ke dauke da kwayar cutar da sauran ruwan jiki. Cutar na yawan kashe mutum idan ba a magance ta ba.

Liberia ta samu mafi yawan wadanda suka harbu da cutar Ebola a fadin duniya.

Fiye da mutane dubu 4 da 800 ne suka mutu cikin shekara guda, inda ake samun sabbin mutane 300 zuwa 400 dake kamuwa da cutar a kowane mako, daidai lokacin da tafi kamari.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

12 + twenty =