Ministan Tsaro ya bukaci ‘yan Najeriya su tunkari mahara

11

Ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi, mai ritaya, ya bukaci yan kasarnan da su fara samun kwarin gwiwar tunkarar ‘yan bindigar dake tayar da zaune tsaye a kasarnan.

Da yake zantawa da manema labarai a jiya a wajen tantance manyan hafsoshin soja da majalisar wakilai ta yi, Bashir Magashi ya bayyana wadanda suka sace dalibai da malaman makarantar sakandiren Kagara a karamar hukumar Rafi ta jihar Neja da cewa matsorata ne.

Yace hakkin yan Najeriya ne su tabbatar da cewa an samu isasshen tsaro a kewaye da su.

Ministan ya kuma yi watsi da rokon da ake yi na a kyale yan kasarnan suke daukar makamai domin kare kawunansu.

Jawabin nasa ya harzuka yan Najeriya musamman a shafukan sada zumunta, inda mutane ke zarginsa da yunkurin mayar da nauyin dake kan masu mulki zuwa kan wadanda ake mulka.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

9 + ten =