Gwamnatin Tarayya tace Najeriya ta fita daga koma bayan tattalin arziki

18

Gwamnatin Tarayya tace Najeriya ta farfado daga koma bayan tattalin arziki bayan kididdigar abinda take samar wa a shekara wato GDP ya kai 0.11 cikin 100 a karshen shekarar 2020.

Karamin Ministan kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Clem Agba, ya sanar da haka jiya a jihar Imo a wajen kaddamar da wani titin mai nisan kilomita 3 da rabi, wanda ma’aikatar aikon gona da cigaban karkara ta tarayya ta gina.

Clem Agba yace an cimma nasarar ne saboda aiwatar da shirye-shiryen dorewar tattalin arziki na gwamanatin tarayya.

Yace a karkashin shirye-shiryen dorewar tattalin arzikin, gwamnatin tarayya ta amince da kudi naira biliyan 34 domin gina titunan karkara 377 a fadin kasarnan.

Yace an kuma amince da jumillar kudi naira biliyan 50 domin bayar da bashi ga manoma a karkashin shirye-shiryen agaji na ma’aikatar aikin gona da cigaban karkara ta tarayya.

Ministan yace titin mai nisan kilomita 3 da rabi, daya ne daga cikin titunan karkara 66 da ma’aikatar aikin gona da cigaban karkara ta tarayya ta kammala zuwa yanzu a karkashin shirye-shiryen dorewar tattalin arziki na gwamanatin tarayya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 × five =