Buhari ya gana da gwamnan Imo dangane da Okorocha

16

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a yau ya gana da gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Hakan yazo ne daga mai taimakawa shugaban na musamman kan harkokin yada labarai, Buhari Sallau, wanda ya wallafa hotunan ganawar.

Duk da cewa har yanzu ba a bayyana cikakken bayanin ganawar ba, amma taron ba zai rasa nasaba da abin da ya faru a jihar Imo ba, wanda aka kama tsohon Gwamnan jihar, Sanata Rochas Okorocha.

An kama Okorocha tare da wasu mukarrabansa a ranar Lahadi bayan kutsa kai zuwa wajen wani gida mallakin matarsa wanda hukumomi suka kwace.

A wani labarin kuma, jam’iyyar PDP ta zargi gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, da tsohon gwamnan jihar, Rochas Okorocha, da laifin mayar da jihar zuwa sansanin yaki.

Kakakin PDP a jihar, Ogubundu Nwadike, a cikin wata sanarwa a jiya yace rikicin tsakanin magoya bayan Okorocha da Uzodimma abin takaici ne.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

seventeen − 5 =