Sojojin Najeriya sun kwato garin Marte

25

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwato garin Marte, bayan sun kashe mayakan ISWAP da Boko Harama da dama, wadanda suka kwace iko da garin.

Wannan na zuwa kasa da sa’o’i 48 na wa’adin da babban hafsan sojan kasa Manjo Janar Ibrahim Attahiru ya ba sojojin na Najeriya su kakkaɓe Boko Haram a yankin na Marte.

Jaridar PRNigeria ta ce sojojin sun kuma tarwatsa nakiyoyin da Boko Haram ta dasa akan hanyoyi domin hana sojoji zuwa garin.

A ranar Lahadin da ta gabata, babban hafsan sojan kasar, Manjo Janar Ibrahim Attahiru ya bayar da wa’adin awanni 48 g dakarun Operation Lafiya Dole su kwato Marte daga hannun Boko Haram.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fifteen − 12 =