Saurayi dan shekara 14 ya harbe wata budurwa ‘yar shekara 15 a Jigawa

78

Wani saurayi mai shekaru 14, Muhammad Sani, ya kashe wata budurwa ’yar shekara 15 a kauyen Damutawa da ke karamar Hukumar Jahun a Jihar Jigawa.

Lamarin ya faru ne a ranar Asabar da misalin karfe 2 na rana lokacin da yarinyar, Habiba Junaidu ta je gidansu Muhammad don siyar da awara.

Yaron ya dauki wata bindiga ta kawunsa da harsasai a ciki, kuma ya harbe ta daga baya. Nan take ta mutu.

Kawun marigayiyar, Umar Damutawa, ya tabbatar da faruwar lamarin ga SkyDaily ta wayar tarho.

Kakakin ‘yan sanda a jihar ta Jigawa, Zubair Aminudeen, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Dutse.

Ya ce bayan samun labarin, ‘yan sanda sun garzaya da budurwar zuwa asibiti inda aka tabbatar da mutuwarta. Zubairu ya ce ‘yan sanda sun cafke wanda ake zargin, sun kwato bindigar, kuma an kama mai ita saboda sakaci, ya kara da cewa har yanzu ana cigaba da bincike.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × 3 =