Yawan mamata a harin rokoki na Boko Haram a Maiduguri sun karu zuwa 16

41

Wani shugaban yan sa kai, Babakura Kolo, ya ce harin Boko Haram a Maiduguri ya kashe mutane 16, ciki har da yara 9 da ke wasan kwallon kafa a wani fili.

Gwamnan jihar, Farfesa Babagana Zulum, a baya ya ce mutane 10 sun mutu yayin da 47 suka jikkata a harin na jiya lokacin da mayakan suka harba rokoki kan birnin da ke da yawan jama’a.

Kungiyar Boko Haram a baya ta yi kutse cikin garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno, ta hanyar amfani da manyan bindigogi da ‘yan kunar bakin wake.

Babakura Kolo ya kara da cewa a daya daga cikin unguwannin da lamarin ya shafa, Gwange, an kashe yara maza 9 lokacin da daya daga cikin rokokin ya sauka a filin da suke kwallon kafa.

Wani dan sa kan, Umar Ari, ya tabbatar da adadin wadanda abin ya shafa, sannan yace adadin na iya karuwa kasancewar mutane da dama sun jikkata.

Wani shaidar gani da ido Sama’ila Ibrahim ya ce mayakan sun tsallaka ramin da ke kewaye da garin Maiduguri, lamari da ya sa mazauna birnin gudun neman tsira

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

14 + 18 =