Dilolin shanu da kayan abinci daga Arewa zuwa Kudu sun fara yajin aiki

2

Dilolin shanu da kayan abinci a karkashin kungiyarsu ta dilolin shanu da kayan abinci ta Najeriya a yau suka tsunduma yajin aiki a fadin kasarnan, biyo bayan karewar wa’adin kwanaki 7 da suka bawa gwamnatin tarayya ta biya musu bukatunsu.

Kungiyar a ranar Lahadi ta gudanar da taron manema labarai inda tace tana neman tsare lafiyar ‘ya’yanta, da biyan kudi naira miliyan dubu 475 na diyyar rayukan ‘ya’yanta da dukiyoyin da akayi asara a lokacin zanga-zangar EndSARS da rikicin kasuwar Shasha.

Kungiyar ta kuma nemi gwamnati da ta bayar da umarnin janye dukka guraren tsayar da ababen hawa a manyan titunan gwamnatin tarayya saboda wahalhalun da yayanta suke sha a lokacin gudanar da ayyukansu.

Uwar kungiyar ta kasa, Hajiya Hauwa Kabir Usman, lokacin da take bayar bahasi a yayin ganawa da manema labarai, ta gargadi yansanda da kada su takurawa yan karta kwana na kungiyar wadanda zasu tabbatar da bin umarnin yajin aiki, wajen ganin cewa babu wani kayan abinci ko shanu da aka kai Kudu daga Arewa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 × three =