Buhari ya sanyawa sabbin hafsoshin soja anini

12

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a yau ya gayawa sabbin hafsoshin soja cewa makonni kalilan aka basu su tsare kasarnan.

Shugaba Buhari yana sa ran kafin faduwar damuna, su samar da tsaro a kasarnan ta yadda manoman da suka tsere daga gonakinsu a sassa daban daban na kasarnan, zasu samu kwarin gwiwar komawa gonakin nasu.

Ya bayar da umarnin jim kadan bayan sanya aninin karin girma kan sabbin hafsoshin soja, a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Ya umarcesu da su zakulo hazakan jami’an sojoji, su aika da su zuwa wuraren da ake rikici domin samun nasara.

Wadanda aka makalawa aninin sun hada da hafsan tsaro, Janar Lucky Irabor, da hafsan sojin kasa, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru, da hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Awwal Zubairu, da hafsan sojin sama, Air Marshal Isiaka Amoo.

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo da sauran manyan jami’an gwamnati, sun halarci bikin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 + sixteen =