Kotu a Kano ta dakatar da mukabala tsakanin Abduljabbar da Malamai

26

Wata kotun majistire a Kano ta dakatar da mukabala tsakanin Abduljabbar Sheikh Nasiru Kabara da malaman addini.

A hukuncinta na yau, kotun ta bukaci dukkan bangarorin da ke shari’ah tsakanin gwamnatin jihar Kano da Abduljabbar Kabar, da su bi umarnin kotu.

Tunda farko, kotun ta haramtawa Abduljabbar Kabar wa’azi da yada koyarwarsa, kafin lokacin da za ta yanke hukunci.

Da yake jawabi kan lamarin, kwamishinan shari’ah na jihar, Musa Lawal, yace a matsayin gwamnatin na mai bin doka, za ta bi umarnin kotu.

An bayar da rahoton cewa an tsayar da ranar 7 ga watan Maris domin mukabalar wacce za a gudanar a fadar mai martaba Sarkin Kano.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

one × two =