Gwamnatin Tarayya zata kashe rabin GDP a bangaren bincike da fasaha

9

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace Gwamnatin Tarayya daga yanzu za take ware rabin abinda take samarwa a shekara wato GDP zuwa bangaren bincike da fasaha.

A cewarsa, matakin wani bangare ne na kokarin gwamnati domin bunkasa cigaban tattalin arzikin kasarnan.

Buhari, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Yemi Osinbajo, ya bayyana haka a jiya yayin bikin bikin bajekolin fasaha da kere-kere na bana.

Wata sanarwa daga hannun mai taimakawa mataimakin shugaban kasa akan yada labarai, Laolu Akande, tace shugaban kasa ya kuma yi jawabi akan kokarin gwamnatinsa cikin yan shekarun da suka gabata, musamman wajen fitar da kudaden kasafin kudin bangaren.

Shugaban kasa yace matakan da aka dauka cikin shekaru sun taimaka wajen kara bincike da fasaha da nufin cimma samun cigaba mai dorewa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two × 2 =