An kashe sama da mutane 50 a kusa da iyakar Mali a Jamhuriyar Nijar

13

Gwamnatin Nijar ta ce mutane 55 sun mutu a wani harin bindiga da aka kai yankin Tilleberi da ke kusa da iyakar kasar da Mali.

Rahotanni sun ce an kai harin ne a jiya Litinin, inda ‘yan bindiga suka bude wuta kan fasinjoji da ke kan hanyar komawa gida daga kasuwa a motar bus. Sannan suka cinnawa motar wuta.

Har yanzu dai babu cikakkun bayanai kan wadanɗa suka kai harin a yankin da ke kudu maso yammacin Nijar.

Sai dai mayakan jihadi sun yadu a yankunan Sahel da dama cikin shekarun baya-bayanan.

Ko a watan Janairu sai da aka kashe akalla mazauna wani kauye su 100 a wani harin masu ikirarin Jihadi.

Gwamnatin Nijar dai ta ayyana zaman makoki na kwana uku daga gobe Laraba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

seventeen − twelve =