Aisha Buhari ta dawo Najeriya bayan watanni 6 a Dubai

18

Uwargidan Shugaban Kasa Aisha Buhari ta dawo kasarnan bayan shafe watanni 7 a Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa.

Majiyoyi sun gayawa manema labarai cewa mai dakin shugaban kasar, wacce ta koma kasar waje da zama bayan bikin auren 1 daga cikin yayanta, Hanan, a halin yanzu tana fadar shugaban kasa da ke Abuja.

An ce ta dawo kasar a jiya da dare.

Ana ta bayyana damuwa dangane da inda take bayan tayi doguwar tafiyar, amma fadar shugaban kasa ta kauracewa magana akan batun.

Babu tabbacin ko ta dawo kasarnan gabadaya ko kuma ta zo Najeriya ne na wucin gadi.

An lura cewa za a kaddamar da litinin da aka rubuta sunan ta, domin karramata, cikin makonni kadan masu zuwa, amma babu tabbacin ko wannan shine dalilin da yasa ta dawo kasarnan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 × three =