KEDCO ya sanar da ragi ga kwastomomin da ya ke bi bashi

11

Hukumar kamfanin rarraba wutar lantarki shiyyar Kano (KEDCO) a jiya ya sanar da ragin da zai yiwa kwastomomi idan zasu biya basukan kudin wutar da ake bin su.

Kakakin kamfanin, Ibrahim Sani Shawai, cikin wata sanarwa, yace kwastomomin da ake bashin naira dubu 20 zuwa dubu 49 da 999, zasu samu ragin kashin 20 cikin 100 idan zasu biya lokaci daya, amma idan zasu biya bashin cikin watanni 2, zasu samu ragin kashi 15 cikin 100.

Yace kwastomomin da ake bashin naira dubu 50 zuwa dubu 99 da 999, zasu samu ragin kashin 20 cikin 100 idan zasu biya lokaci daya, amma idan zasu biya bashin cikin watanni 2, zasu samu ragin kashi 25 cikin 100.

Ya kara da cewa wadanda ake bin bashin naira dubu 100 zuwa dubu 199 da 999, zasu samu ragin kashi 45 cikin 100 idan zasu biya lokaci daya, amma idan zasu biya bashin cikin watanni 2, zasu samu ragin kashi 35 cikin 100.

Ibrahim Shawai yace wadanda ake bin bashin kudi fiye da naira dubu 200, zasu samu ragin kashi 55 cikin 100 idan zasu biya lokaci daya, amma idan zasu biya bashin cikin watanni 2, zasu samu ragin kashi 45 cikin 100.

Yayi bayanin cewa wannan garabasar zata kare ne cikin wata guda.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 + seven =