‘Yan bindiga sun kashe mutum guda da sace wasu 2 a Jigawa

39

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe wani mutum mai suna Sabo Yusuf dan shekara 25 tare da sace mahaifiyarsa da kaninsa a karamar hukumar Birnin kudu da ke Jihar Jigawa.

An gano cewa yan bindigan sun afka gidan Alhaji Abubakar dake Kawo Quaters a cikin garin Birnin Kudu, suka kashe daya daga cikin yayansa sannan suka tafi da daya daga cikin matansa da kuma wani yaro dan shekaru takwas.

Kakakin ‘yansandan jihar nan, Zaharaddeen Aminudeen ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Dutse.

Ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 3 na safiyar yau a garin Birnin kudu, inda wasu mutane da ba a san ko su waye ba suka kai hari suka harbi wani mutum a kirjinsa sannan suka tafi da matarsa da wani dan nasa zuwa wani wurin da ba a sani ba.

Aminudeen ya ce yan sanda sun garzaya da wanda lamarin ya rutsa da shi zuwa Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Birnin Kudu kuma likita ya tabbatar da cewa ya mutu.

Ya ce ‘yan sanda na kokarin ganin sun ceto wadanda aka sace tare da cafke masu laifin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

17 − 8 =