Gwamnatin Tarayya ta ciyo bashin Dala Miliyan Dubu domin tallafawa yan kasuwa

4

Bankin Masana’antu a karkashin kulawar Ma’aikatar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, ya samu nasarar ciyo bashin dala miliyan dubu 1, kwatankwacin naira miliyan dubu 411, domin agazawa kananan da matsakaitan yan kasuwa a kasarnan.

Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Adeniyi Adebayo, ya sanar da haka a jiya, a wajen shirin karawa juna sani kan tallafin da ake bawa yan kasuwa, wanda aka gudanar a Abuja.

Adebayo a wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman akan yada labarai, Ifedayo Sayo, yace bashin zai taimakawa kokarin bankuna wajen tallafawa kananan da matsakaitan yan kasuwa kamar yadda ya kamata, a manyan bangarorin tattalin arzikin Najeriya.

Adebayo yace bashin, wanda za a aiwatar da shi da hadin gwiwar abokan hulda na kasa da kasa, za a biya shi cikin lokaci mai tsayi.

A cewarsa, hakan wani bangarene na kokarin gwamnatin tarayya wajen farfado da tattalin arziki da dorewar cigaba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 × five =