Bashin da ake bin Najeriya ya karu zuwa naira tiriliyan 32.29

19

Yawan basukan da ake bin kasarnan da suka hada da na gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihoshi, ya kai naira tiriliyan 31 da biliyan 290 zuwa ranar 31 da watan Disambar bara, daga naira tiriliyan 32 da biliyan 220 a ranar 30 ga watan Satumbar bara, a cewar hukumar kididdiga ta kasa (NBS).

Yawan basukan da ake bin kasarnan a waje sun kai naira tiriliyan 12 da biliyan 710, wato kashi 38.6 cikin 100, yayin da wanda ake bin kasarnan a cikin kasa ya kai tiriliyan 20 da biliyan 210, wato kashi 61.4 cikin 100.

Kamar yadda yazo a rahoton hukumar na basukan cikin kasa da na waje na karshen shekarar 2020, wanda aka wallafa a shafin internet na hukumar, jumillar bashin da ake bin jihoshi da babban birnin tarayya ya kai naira tiriliyan 4 da biliyan 190, inda jihar Lagos ke da adadi mafi yawa da kashi 12.15 na bashin, yayin da Jigawa ke da adadi mafi karanci da kashi 0.74 cikin 100 na bashin.

Rahoton ya kuma nuna cewa an ciyo bashin dala biliyan 17 da miliyan 930 daga hukumomin kasa da kasa, yayin da aka ciyo bashin dala biliyan 4 da miliyan 60 daga wasu kasashe.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

17 + 13 =