Buhari ya ce rayuwar yan Najeriya ta fi karko idan ana tare

6

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gargadi masu san raba kasarnan da cewa ‘yan Najeriya sun fi samun cigaba idan suna tare.

Shugaban Kasar ya sanar da cewa ban da rikice-rikicen da aka samu a tarihin kasarnan lokaci zuwa lokaci, wadanda ke da alaka da banbancin kabila da al’ada da yare da kuma addini, duk da hakan, rayuwar yan Najeriya ta fi armashi da inganci a zaman da ake yi tare da juna.

Buhari ya fadi haka a lokacin da ya jagoranci taron taya murnar cika shekara 69 ga jagoran jam’iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, ta intanet daga fadarsa ta shugaban kasa da ke Abuja.

Tsohon gwamnan Legas kuma tsohon sanata, Bola Ahmed Tinubu na gudanar da taron bikin ne a Fadar Gwamnatin Jihar Kano a yau.

Jagoran matasa da ya nada kansa, Sunday Igboho, da tsohon shugaban tsagerun Neja Delta, Asari Dokubo, na daga cikin wadanda a yan kwanakinnan suke neman a raba kasarnan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 × 3 =