IPOB sun kashe Hausawa yan kasuwa 13

34

Wasu da ake zargin ‘ya’yan kungiyar masu fafutukar neman kasar Biafra ne (IPOB) sun kashe Hausawa yan kasuwa su 13 cikin mako guda a jihoshin Imo da Enugu.

An kuma kashe jami’an yansanda da dama da cinnawa gine-gine wuta a hare-haren da ke kara yawaita akan jami’an tsaro a yankunan kudu maso gabas da kudu maso kudu.

A harin baya-bayannan kan fararen hula yan Arewa, wasu yan bindiga sanye da kakin soja lokacin da suka kai farmaki zuwa kasuwar Afor Umuaka sun bindige wasu mahauta Hausawa 4 a ranar Asabar da misalin karfe 8 da rabi na dare.

A Enugu, ranar Litinin da ta gabata, akalla mutane 6 aka kashe a lokacin wani hari da aka kai kauyen Adani a yankin karamar hukumar Uzo-Uwani ta jihar Enugu.

Daya daga cikin wadanda aka kashe, shahararren dan kasuwa ne Bahaushe, wanda aka ce yana zaune a wajen tsama da shekaru 30.

Rundunar yansandan jihar ta tabbatar da harin amma ta ki cewa uffan dangane da yawan wadanda aka kashe.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 + fifteen =