‘Yan bindiga sun farwa ‘yansanda da fitar da fursunoni a Imo

10

‘Yan bindiga da ake zargin ‘ya’yan kungiyar masu fafutukar neman kasar Biafra ne (IPOB) sun cinna wuta a wasu bangarorin helkwatar rundunar yansandan jihar Imo tare da kai hari zuwa gidan yarin Owerri, babban birnin jihar.

An gano cewa yan bindiga sun ci karfin jami’an tsaron da ke ofishin yansandan da gidan kason.

‘Yan bindigar sun kuma kai farmaki zuwa ofishin sashen binciken manyan laifuka na CID da ke rundunar yansandan jihar Imo, kuma suka fitar da wasu da ake tsare da su.

Maharan sun kone kusan dukkan motocin da aka ajiye a helkwatar yansandan.

‘Yan bindigar, wadanda aka ce sun zo a cikin motoci sama da 10, sun kuma kai hari kan sojojin da aka ajiye a Umuorji, akan babbar hanyar Owerri zuwa Onitsha.

Da aka nemi jin ta bakinsa, kakakin yansanda na jihar, Orlando Ikeokwu, ya tabbatar da hare-haren.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

18 + eleven =