Sama da fursunoni 80 ne suka koma gidan yari

25

Akalla fursunoni 80 ne suka mayar da kansu zuwa gidan yarin Owerri bisa radin kashin kan su.

Sama da fursunoni dubu 1 da 844 ne suka tsere a ranar Litinin lokacin da yan bindiga suka kai hari gidan yarin tare da sakinsu.

Yan bindigar sun kuma kai hari zuwa helkwatar yansandan Najeriya tare da cinna wuta kan ofishin sashen binciken manyan laifuka, bayan sun saki dukkan wadanda ake tsare da su.

A ziyararsa zuwa guraren da aka lalata a jiya, ministan cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, yace fursunonin da suka koma da kansu, baza a tuhumesu da fasa gidan yari ba.

An gano cewa akalla mutane 40 ne suka dawo a jiya, wanda ya kawo jumillar fursunoni 82 da ake tsare da su a halin yanzu.

Jami’in hulda da jama’a na gidan yarin, Joe Madugba, ya gayawa manema labarai cewa fursunonin sun dawo tsakanin jiya zuwa yau.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

seven + ten =