Amurka ta ce dakarunta za su fice da ga Afghanistan nan da 11 Satumba

12

Amurka za ta janye dukkan dakarunta daga Afghanistan zuwa ranar 11 ga watan Satumban wannan shekara, shekaru ashirin daidai tun bayan harin 11 ga watan Satumbar 2001.

Jami’an Fadar White House sun ce nan gaba Shugaba Biden zai gabatar da shirin janye sojoji daga abin da ya zama yakin Amurka mafi tsawo.

Wasu sanatocin Republican sun soki janyewar da ake shirin yi a matsayin ja da baya kafin samun nasara a kan abokan gaba.

Jinkirin na iya yin barazana ga tattaunawar zaman lafiya tsakanin Amurka da Taliban da kuma gwamnatin Afghanistan da za a yi a Turkiyya a cikin wannan watan.

Jami’an Amurka da na NATO sun ce har yanzu kungiyar Taliban ba ta cika alkawurran da ta dauka na rage tashin hankali ba.

An gargadi ‘yan Taliban da cewa idan suka kai wa sojojin Amurka hari a lokacin da ake janyesu, za su gamu da martani mai zafi.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

10 + 15 =