Jakadan Najeriya a Morocco ya kama aiki a yau

155

Jakadan Najeriya a kasar Morocco, Ambassada Ibrahim Saleh, ya kama aiki a yau a Rabat, babban birnin kasar.

Jakadan ya hori abokan aikinsa a ofishin jakadancin da su tabbatar da dorewar kyakykyawar alaka tsakanin Najeriya da Morocco domin amfanin kasashen biyu.

Daga nan, ya zagaya ofishin jakadancin inda ya tabbatarwa da ma’aikata cikakken goyon bayansa da jajircewarsa wajen jin dadinsu.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar 16 ga watan Fabrairun 2021, a lokacin taron kaddamar da wadanda aka nada jakadun kasashe, ya bukaci sabbin jakadun Najeriya da su zama jakadun kasar nagari tare da jawo masu zuba jari zuwa Najeriya daga kasashen da suke aiki.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 × 4 =