Buhari ya amince da kafa hukumar takaita yaduwar kananan makamai

19

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da kafa hukumar takaita yaduwar kananan makamai a kasarnan.

A sanarwar da mai taimaka wa shugaban kasar kan shafukan sada zumunta, Bashir Ahmad, ya wallafa a shafinsa na Twitter yau Litinin, ya ambato mai magana da yawun ofishin mai ba Buhari shawara kan sha’anin tsaro yana cewa hukumar za ta kasance a ofishinsu.

Hukumar za ta maye gurbin kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar kananan makamai, in ji sanarwar.

A cewar sanarwar kafa hukumar na cikin matakan inganta tsaron kasarnan, domin magance barazanar tsaro da kuma karfafa shirin da kasashen yankin ke yi, wajen takaitawa da magance matsalar yaduwar kananan makamai.

A baya dai Shugaba Buhari ya sha kokawa kan karuwar kananan makamai da ma manya cikin kasarnan, lamarin da ya ta’allaka da yakin da aka yi a kasar Libya.

Hukumomi sun bayyana cewa akwai dubban kananan makamai a hannun ‘yan kasar, abin da ke ta’azzara hare-hare da kuma yin barazana ga zaman lafiya a kasarnan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

sixteen − nine =