Buhari ya soke ziyarar Sallah zuwa fadar shugaban kasa

16

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin takaita dukkan bukukuwan Sallah mai zuwa saboda annobar corona.

Sanarwar hakan tazo ne cikin wata sanarwa a yau ta hannun Mallam Garba Shehu, babban mai taimakawa shugaban kasa akan kafafen yada labarai da huldar jama’a.

Garba Shehu ya kuma sanar da cewa babu ziyarar Sallah zuwa ga shugaban kasa kamar yadda aka saba bisa al’ada, daga wajen shugabannin addinai da na al’umma da yan siyasa, bayan saukowa daga Sallah.

Kakakin na shugaban kasa ya kuma raiwato shugaban kasa na godewa malaman addinin musulunci da dukkan shugabannin addini wadanda ke addu’o’in zaman lafiyar kasarnan da mutanenta.

Shugaba Buhari yayi kira ga dukkan jagororin al’umma da su tattauna da matasansu tare da gargadinsu akan kauracewa yin amfani dasu wajen tayar da rikici.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

nineteen − 18 =