Mutane 21 sun mutu bayan Isra’ila ta cigaba da luguden wuta a Gaza

14
A view shows the site of an Israeli air strike amid a flare-up of Israel-Palestinian violence, in Gaza City May 11, 2021. REUTERS/Suhaib Salem

Ma’aikatar lafiyar kasar Falasdinu tace akalla Falasdinawa 21 aka kashe a hare-haren saman Isra’ila kan Zirin Gaza, bayan kungiyar Hamas ta kaddamar da hare-haren rokoki zuwa Isra’ila.

Ma’aikatar lafiyar Gaza ta gayawa manema labarai a jiya cewa mutane 21, ciki har da yara, aka kashe a hare-haren.

An kaddamar da hare-haren bayan kungiyar Hamas ta harba rokoki da dama zuwa Isra’ila, biyo bayan karewar wa’adin da kungiyar ta bai wa Isra’ila na ta janye dakarunta daga masallacin Al Aqsa dake Jerusalam.

Tunda farko a jiya, zaman dardar a harabar masallachin, na uku mafi tsarki a Musulunchi wanda kuma Yahudawa ke girmamawa, ya karu inda aka raunata Falasdinawa sama da 300 lokacin da yansandan Isra’ila suka mamaye masallachin suna harba harsasan roba, nakiyoyi da hayaki mai sa hawaye.

Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya gudanar da zaman ganawar gaggawa dangane da rikicin na Jerusalam, inda shugabannin duniya ke kiran a kawo karshen tashin-tashinar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

one × two =