Yansanda sun ceto masallata 30 da aka sace a masallachi a Jibia

20

Rundunar ‘yansandan jihar Katsina ta ce ta ceto masallata 30 da wasu da ake zargin ‘yan fashin daji ne suka sace daga masallaci.

An ruwaito yadda ‘yan fashin suka kai hari a masallacin da ke Jibiya inda masallatan suka taru don yin Sallar Tahajjud.

An ce wasu matasa da kungiyoyin ‘yan kato da gora a garin sun shirya domin tunkarar ‘yan ta’addan idan za su kawo musu hari, amma ‘yan fashin sun bi ta wata hanyar ta daban don samun damar shiga garin.

Da yake magana da manema labarai game da lamarin, kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Katsina, Gambo Isah, ya ce ‘yansanda tare da sojoji da sauran kungiyoyin ’yan kato da gora sun bi bayan ‘yan bindigan tare da kubutar da 30 daga cikin masallatan.

Yace bayan an kidaya su, an gano cewa har yanzu ba a samu 10 daga cikin masallatan ba.

Gambo Isah ya kara da cewa ‘yansanda suna kokarin hada kai da iyalan da masu garkuwar suka tuntuba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

9 + 19 =